PDP Ta Kafa Kwamitin Mutane 14 Kan Sasanta Rikicin Atiku Da Wike
Sakamakon wata ganawar sirri da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da Gwamna Jihar Rivers Nyesom Wike Suka yi, Jam’iyyar ta samu nasarar kafa kwamitin mutane 14 da za su tuntuɓa gami da bayar da shawara ga dukkanin ɓangarorin biyu.
Wata Majiya a jam’iyyar wadda ke da bayanai kan lamarin ta shaida cewa har yanzu ba bu bayanai ka Mambobin Kwamitin, a dalilin har yanzu ba a sanar da wasu daga cikinsu a hukumance ba.
Majiyar wadda ta nemi a ɓoye sunanta saboda babu izinin yin magana da Manema Labarai, ta bayyana cewa ana sa ran kwamitin zai fara aiki da gaggawa.
Jam’iyyar PDP ta fada cikin rikici tun bayan da Alhaji Atiku Abubakar ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2023.
Wannan lamari ya saɓawa tunanin da wasu ke yi na cewa Wike ne zai zaɓa ganin cewa shine yazo na biyu a zaɓen Fidda Gwani wanda Atiku ya zama Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa.
