Ƴan sanda Sun Kama Ɗan Takarar Sanatan Borno,Sun Kulle Hedikwatar NNPP
Gwamnatin jihar Borno ta rufe hedikwatar jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na jihar da ke Maiduguri babban birnin jihar.
Daily Trust ta ruwaito cewa, an ta rufe hedikwatar jam’iyyar tare da wasu ofisoshinta a ranar Alhamis.
Dan takarar gwamnan jihar Borno a karkashin jam’iyyar NNPP, Dakta Umaru Alkali, ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri.
Ya kara da cewa an kama dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar na Borno ta tsakiya, Hon Attom Muhammad Maigira, bayan da ya amsa gayyatar ‘yan sanda.
