Babu Abinda APC Zata Gayawa Ƴan Najeriya Su Yarda Da’ita – PDP

Jam’iyyar PDP ta ce jam’iyyar APC mai mulkin kasa ba ta da wani abin nunawa ga ‘yan Najeriya.

Daraktan yakin neman zaben PDP na matasa a Jigawa, Malam Umar Danjani ya bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani ga kungiyar matasan APC.

Ya ce jam’iyyar PDP ce kadai a Najeriya da ta aiwatar da ayyukan raya kasa da ‘yan Najeriya ke alfahari da su.

A cewarsa “Gwamnatin APC ba ta da wani abu da za ta nunawa ‘yan Najeriya baya ga talauci da rashin tsaro da rashin shugabanci.”

Ya ce jam’iyyar APC tana cikin firgici kan karbuwar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da dan takarar gwamna a jihar Jigawa, Mustapha Sule Lamido.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *