Majalisar Dattawa Ta Fara Binciken Shirin Samar Da Ayyukan Jama’a Na Biliyan 52
Kwamitin majalisar dattijai da ke kula da asusun gwamnati a ranar Talatar nan ya fara binciken shirin ayyuka na musamman na Naira biliyan 52 da gwamnatin tarayya ta aiwatar a shekarar 2020.
Shirin wanda hukumar kula da ayyukan yi ta kasa karkashin kulawar karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi aka yi shi.
Shirin dai an yi niyya ne da daukar matasa marasa sana’a 1,000 aiki a kowace kananan hukumomin kasar nan 774 na tsawon watanni uku.
Ana sa ran wadanda suka ci gajiyar shirin za su gudanar da ayyukan yi wa jama’a hidima tare da karbar alawus na Naira 20,000 duk wata.
Mambobin kwamitin, a wani zaman bincike a ranar Talatar, sun gano cew Naira biliyan 26 daga cikin jimillar Naira biliya 52 da aka kashe kan shirin, an same su ne daga Service Wide Vote.
Kwamitin yana binciken Naira tiriliya 5 Service Wide Votes da hukumomi 252 suka kashe daga 2017 zuwa 2021.
Sanata Thompson Sekibo (PDP, Rivers) da Michael Nnachi (PDP, Ebonyi) sun yi zargin cewa babu daya daga cikin mazabarsu da ya ci gajiyar shirin.
Kwamitin ya umurci NDE da ta gabatar da cikakken rahoto kan wadanda suka ci gajiyar shirin a jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Kwamitin ya bukaci hukumar ta mika sunaye, lambobin waya, da bayanan asusun mutane 774,000 da suka ci gajiyar tallafin.
