Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Gwamna Ifeanyi Okowa ya yi kira ga takwaransa na jihar Ribas, Gwamna Nyesom Wike kan bukatar a yi sulhu na gaskiya a kan batutuwa masu da ke dagula jam’iyyar.
Mista Okowa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar sirri da Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a masaukin gwamnatin jihar Benue da ke Asokoro, a Abuja.
Ya kara da cewa, jinkirin da aka samu na ganawa da Gwamna Wike, ya biyo bayan tafiyar sa ne zuwa kasar waje, kuma a yanzu da ya dawo jam’iyyar da dan takararta na shugaban kasa za su yi duk mai yiwuwa don ganin sun sasanta da shi.
Majiyar Jaridar Jakadiya ta rawaito cewa, A nasa bangaren, Ortom ya ce shawarar da ya bayar kan bukatar gamsar da Gwamnan Jihar Ribas ita ce hanya mafi dacewa da a bi.
Ya ce ya na bayan yunkurin sasantawa da Wike domin maslahar jam’iyyar baki daya domin dole ne dukkan hannaye su kasance a dun kule kafin zaben 2023 mai zuwa.
