Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta IHRC-RFT ta yi alla-wadai da tashin farashin mai a Najeriya

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta ƙasa da ƙasa, wato International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC-RFT), ta bayyana matuƙar damuwarta kan ci gaba da tashin farashin man fetur a Najeriya, tare da irin wahalhalun da hakan ke jefa talakawan ƙasa.

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da Ambasada Abdullahi Bakoji Adamu
Daraktan ƙasa
na IHRC-RFT ya fitar.

Ƙungiyar ta bayyana cewa duk da cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke da albarkatun mai masu yawa tare da damar tace shi a cikin gida, har yanzu ‘yan ƙasa na ganin abin mamaki yadda farashin mai ke ci gaba da ƙaruwa.

Ta ce wannan lamari ya haddasa tsadar sufuri, tashin farashin abinci, da kuma ƙaruwa a tsadar rayuwa a faɗin ƙasar.

IHRC-RFT ta ƙara da cewa duk da sauye-sauyen da ake samu a farashin mai a kasuwannin duniya, ‘yan Najeriya na sa ran albarkatun ƙasar za su kawo sauƙin rayuwa da riba ga al’umma baki ɗaya. Sai dai, akasin hakan ne ke faruwa, inda tashin farashin mai ke ƙara jefa iyalai cikin matsin tattalin arziki.

Ƙungiyar ta yi kira ga shugabannin ƙasa da su ɗauki matakan gaggawa cikin gaskiya da riƙon amana domin kare jin daɗin ‘yan ƙasa. Haka kuma ta buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki, musamman ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa, da su duba lamarin da kyau tare da ɗaukar matakan da suka dace domin magance wannan matsala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *