Gwamnatin Jihar Kano ta rusa wasu gine-gine da aka yi ba tare da izini ba a yankin Sharada da ke karamar hukumar Gwale, tare da gargadin cewa za a gurfanar da masu hannu a lamarin.
Kwamishinan kasa da tsare-tsare , Abduljabbar M. Umar, ya ce an gano wasu mutane suna gina shaguna da wasu gine-gine a filin da aka ware domin wurin shakatawa na mazauna yankin hukumar gidaje ta tarayya (FHA).
Ya bayyana cewa gwamnati ba za ta amince a mayar da filin zuwa wajen kasuwanci ba, yana mai jaddada cewa duk wani gini dole ne ya samu amincewar hukumar tsara birane.
Umar ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da sanya ido a yankin tare da mayar da filin wurin shakatawa domin amfanin al’umma.