Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Alhamis 19 da Juma’a 20 ga watan Maris, 2026 a matsayin ranakun hutu domin bikin Eid-el-Fitr, wanda ke nuna ƙarshen watan azumin Ramadan.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya.
A wata sanarwa da Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Talata, ministan ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara.
Ya kuma bukaci Musulmi da su ci gaba da riko da kyawawan dabi’u na soyayya, karamci, zaman lafiya, haƙuri da sadaukarwa da aka koya a watan azumi.
Tunji-Ojo ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin bukukuwan wajen yi wa ƙasa addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.
Yayin da ya yi wa Musulmi fatan murnar Eid-el-Fitr cikin farin ciki, ya bukaci jama’a da su gudanar da bukukuwan cikin natsuwa tare da taimaka wa marasa galihu.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin dukkan ‘yan Najeriya.
