An rantsar da Soludo karo na biyu a matsayin Gwamnan jihar Anambra

Gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya sake karɓar rantsuwa domin fara wa’adi na biyu a kan kujerarsa.

Haka kuma, mataimakinsa Onyekachukwu Ibezim ya sake karɓar rantsuwa domin sabon wa’adi a matsayin mataimakin gwamna.

Soludo ya samu nasara a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a watan Nuwamban 2025, inda ya kada babban abokin hamayyarsa Nicholas Ukachukwu na jam’iyyar APC.

An gudanar da bikin rantsuwar ne a ranar Talata a birnin Awka, babban birnin jihar, tare da halartar manyan baki daga sassa daban-daban.

Daga cikin wadanda suka halarta akwai mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da tsoffin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.

Bikin ya kuma samu halartar manyan ‘yan siyasa, jami’an gwamnati, magoya baya da kuma sarakunan gargajiya, wanda ke nuna fara sabon wa’adi na shekaru hudu ga gwamnan.

A cikin jawabin da ya gabatar bayan rantsuwa, Soludo ya yi alkawarin cika dukkan alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.

Ya bayyana cewa sake zabensa wata gagarumar amincewa ce da manufofinsa, yana mai jaddada cewa ba za su dauki goyon bayan al’ummar jihar da wasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *