Ƴan Ta’addan Boko Haram Sun Mutu A Ruwa, Bayan Ruwan Bama-Baman Soji

Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.

Sama da Ƴan Ta’addan Ƙungiyar Boko Haram 70 sun mutu a ruwa, biyo bayan fatattakar da jami’an Sojin sama na Operation Hadin Kai suka yi masu a jihar Borno, Inji wasu Majiyoyi.

Tun da farko dai an gano cewa jami’an soji hadin gwiwa da ƴan kungiyar Sa Kai a ranar Alhamis sun kashe sama da ƴan Boko Haram 20 a kauyen Sheruri dake karamar hukumar Bama ta Jihar Borno a ranar Alhamis.

Majiyoyi sun bayyana cewa, bayan harin Sheruri, wadanda suka tsere sun mutu cikin Kogi dake tsakanin kauyen Dipchari na ƙaramar hukumar Bama a ranar Juma’a.

“Mayaƙan sun gamu da gamonsu, inda suka rasa sama da Mayaƙa 70 a ƙauyen Dipchari. Har yanzu ba’a gano sauran ba kamar yadda nake maku jawabi,” Inji wata Majiya ta Jami’an tsaro.

Wata Majiyar ta bayyanawa wakilin Majiyar mu cewa bayan faruwar lamarin an ga Ƴan Ta’addan suna ceto gawarwakin matattun ƴan uwansu a Kogi.

“Da safiyar nan da misalin Karfe 8:30 sun gudanar da Sallar Jana’iza na Mayaƙan Boko Haram sama da 50 a kauyen Dipchari yanzu haka suna cigaba da binciken sauran yan ta’addan.

“Sun gano gawarwaki da dama daga cikin ruwan amma kuma an rasa wasu gawarwakin na Mayaƙan Boko Haram,” Inji Majiyar.

Har zuwa kammala wannan rahoton babu wani bayani daga hukumar tsaro a Hukumance, amma da yawan mutanen yankin sun tabbatar da faruwar hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *