Daga Wakiliyar Mu Amira Salisu Batsari
A yayin da babban zaben shekarar 2023 ke kara matsowa, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa Farfesa Mahmood Yakubuz yayi kira ga jam’iyyun siyasa da yan takarar su dasu maida hankali kan gangamin zabe.
Farfesa Yakubu yayi kiran ne a lokacin wani taron “masana kan yadda za’a gudanar da zabe a cikin tsaro” da cibiyar Kula da cigaban Dimokuraɗiyya (CCD) Haɗin gwuiwa da Hukumar, wanda aka gudanar a Otel na Transcorp Hilton dake Abuja.
Ya bayyana cewa, “kamar yadda za’a fara yawon gangamin yaƙin neman zaɓe, muna rokon dukkanin jam’iyyu da kuma yan takara dasu mayar da hankali kan yaƙin neman zaɓe. wannan hanyar itace mafi kyau da zasu marawa ƙoƙarin mu baya na tabbatar da Sahihin zaɓe, wanda Ƙuri’un da Ƴan Ƙasa suka kaɗa su zasu tabbatar da wanda yaci zaɓe.
Ya kara da cewa taron yana da .. saboda yanayin rashin tsaro dake faruwa a wasu sassan kasar nan da kuma hadarinsa a zaben mai zuwa.
“Lokaci yayi saboda zaben na kara matsowa amma har yanzu akwai lokacin da za’a gabatar da tsaro dangane da zaben.
Shugaban hukumar zaben ya bayyana cewa hukumonin tsaro zasu taimakawa mutane domin yin zabe lafiya.
