Na Fito Takarar Gwamna Ne Saboda Mawuyacin Halin Da Jahar Katsina Ta Ke Ciki – Nura Khalil

*JIHAR KATSINA TANA CIKIN MAWUYACIN HALI*

Halin da ake ciki na samar da ababen more rayuwa da tattalin arzikin jihar Katsina ya zama abin damuwa ga dan takarar gwamnan jihar Katsina Eng Nura khalil.

Dan takarar Gwamnan na jam’iyyar NNPP, watau jam’iyya mai kayan dadi Eng Nura khalil, bayan zantawa da yayan jamiyyar ta NNPP ya shaida masu cewa ni na shiga takaran siyasa ne “ba don son kai ba”, sai dan mawuyacin halin da jihar katsina take ciki. Ko ina ansamu koma baya kuma jiharmu tana bukatar a ceto ta daga cikin wannan annobar da aka jefata a ciki.

A cewar Eng Nura khalil gwamnati mai ci yanzu ta gaza kare mutunci da kimar al’ummar da suka zabeta, babu wani aikin ci gaba da gwamnatin take aiwatarwa a jihar ta katsina, duba da rashin biyan albashi akan lokaci da kuma rashin abubuwan more rayuwar yan jihar.

Ya kara da cewa idan Allah ya bashi ikon kafa gwamnati a jihar ta katsina za mu biya albashi akan lokaci kuma zamu samar da hanyoyin samun kudin shiga ga jiharmu ta katsina domin amfanuwar al’umma ba kuma zamu dogara da kudin da ake turowa daga Abuja ba.

Eng Nura khalil yace jiharmu ta katsina tanada albarkatu da yawa wanda Allah ya albarkace ta dasu musamman harkar noma, zamu inganta fannin noma da kiwo muyima sauran jihohin kasarnan zarra, zamuyi aikin da ya dace na dawo da hayyacin jihar katsina.

Idan muka sami Nasara ba nasarar kaina ba ce ni kadai. Nasara ce ta kowa da kowa a jihar katsina baki daya. Domin za’a sami, wakilci mai inganci da kuma cin ribar dimokuradiyya ga al’umma jihar katsina.

Eng Nura khalil yakara da cewa jam’iyyar NNPP zata kawo ci gaba mai dorewa a jihar ta katsina, zamu kawo sauyin da zai inganta rayuwar al’umma, ina mai tabbatar da cewa ba zamu bawa al’ummar jihar Katsina kunya ba, Eng Nura khalil ya ce ina matukar damuwa da halin da ake ciki a jihar Katsina ina matukar kishin ganin an samar da shugabanci na gari, Eng Nura khalil ya yi imanin cewa abin da jihar Katsina ke matukar bukata a halin yanzu shi ne shugaban da zai fitar da al’umma daga kangin bauta da kuma mulkin kama-karya. Babu fensho, babu gratuity, ba albashi, musamman ma Malaman firamare, da ma’aikatan kananan hukumomi suna shan wahala, ba za mu iya samun ci gaba ba muddin ana zaluntar al’umma.

Eng Nura khalil yayi kira da al’ummar jihar Katsina da su fito baki daya su zabi jam’iyyar NNPP a zabe mai zuwa domin kawar da azzalumar gwamnatin dake ci yanzu, gwamnati ce mai wawaso da watanda da kudin alumma a cewarsa.

Ku fito dukanku kuyi aikin jihadin kawar dasu, ku hukunta su da katin zabenku ta hanyar chanjasu a wannan zaben mai zuwa.

Yakara da cewa ni da Eng Muttaka Rabe Darma mun himmatu wajen kawo sauyi mai dorewa a rayuwar mutane da dama ta hanyar da’a da dabi’unmu, wanda ke cike da tausayin Al’umma da kuma ayyukan alherin da muka aiwatar a fadin jihar katsina.

Mutane marasa son kai da kishin jama’a ne kawai za su iya kawo murmushi a fuskokin jama’a ta hanyar gudanar da mulki na gari, burinmu shi ne samar da jihar Katsina da za ta yi aiki ga kowa da kowa; ba wai ga wadanda ke cikin jihar kadai ba, har ma da daukacin ‘yan Nijeriya mun fahimci cewa, tattalin arzikin Nijeriya gaba dayansa ya dogara ne da jihohi masu arzikin man fetur mu kuma zamu nuna cewa harkar noma da kiwo zata kawo sauyi kuma hakan ya sa muka zama ‘yan takarar gwamna a jiharmu ta Katsina mai albarka.

Zamu mayar da hankali wajen yi wa al’umma hidima da kuma kyautata fannin ilimi, Kiwon lafiya, samar da ruwan sha, da kuma inganta harkar noma, samar da ababen more rayuwa ga kowa da kowa, samar da ayyukan yi ga wadanda basada aiki domin su dogara da kawunansu, ayyukan bunkasa matasa da sauran ababen more rayuwa, jiharmu zata dogara da kanta bazamu jira kudi daga Abuja ba.

A karshe yayi addu’a ga jihar ta katsina tare da fatan Allah ya zaunar da jihar ta katsina lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *