2027: Ba wani dan takarar jam’iyyar adawa da zai iya kayar da Tinubu a Abuja – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa zai yi matuƙar wahala ga kowanne ɗan takarar adawa ya kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 a Abuja.

Wike ya faɗi hakan ne bayan rangadin duba ayyukan raya ƙasa da ake yi a garuruwan karkara na Abuja, inda ya ce manyan ayyukan more rayuwa da ake aiwatarwa suna sauya rayuwar al’umma, tare da inganta sufuri da damar tattalin arziki.

Ya bayyana cewa gwamnati ta sauya salo daga mayar da hankali kan tsakiyar birni kaɗai, zuwa bunƙasa yankunan karkara domin su ma su amfana da ci gaban gwamnati.

Ministan ya nuna cewa sabbin hanyoyi da ayyukan gine-gine a wurare kamar Karu da Kubwa na taimakawa rage wahalar zirga-zirga, inda yanzu ake iya yin tafiya daga Kuje zuwa tsakiyar Abuja cikin sauƙi.

Sai dai ya lura cewa a zaɓen 2023, Peter Obi na jam’iyyar Labour Party ne ya lashe zaɓe a Abuja, inda ya doke Tinubu da kuma Atiku Abubakar.

Duk da haka, Wike ya ce yanayin siyasa a Abuja na canzawa sakamakon ci gaban da ake samu a fannin ababen more rayuwa da ayyukan gwamnati, wanda ya ce zai ƙara wa Tinubu goyon bayan jama’a a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *