2023: Mulkin Muslumi-Kirista Bai Kaimu Ko’ina Ba, Don Haka Tinubu Yayi Dai-dai — Oshiomhole

2023: Mulkin Muslumi-Kirista Bai Kaimu Ko’ina Ba, Don Haka Tinubu Yayi Dai-dai — Oshiomhole

Tsohon Gwamnan Jahar Edo, Kuma Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya magantu akan zaɓin Musulmi a matsayin abokin Takara da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ahmed Bola Tinubu yayi.

Oshiomhole yace yanzu lokaci ne da ƙasar zata Watsar da batun Son kai da suka ƙunshi, Addini, kabilanci, tare da maida hankali akan nagartar Ɗan Takarar domin cigaban Ƙasar.

Da yake jawabi a gidan Talabijin na TVC a ranar Alhamis, tsohon Gwamnan ya bayyana gamsuwar da Takarar Musulmi da Musulmi yana mai yabawa Tinubu kan zaɓin.

Tinubu dai ya zaɓi tsohon Gwamnan Jahar Borno Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar sa.

Yace “yanda abokanan hamayya suke cigaba da sukar Takarar Musulmi da Musulmi, shiyasa na ƙara yarda cewa Asiwaju yayi zaɓi mai kyau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *