Daruruwan matane Maza da Mata sun fito zanga zanga a Kaduna a Kaduna, sun nemi a hukunta El-Rufai.

Daruruwan matasa da suka bayyana kansu a matsayin ƴan kishin ƙasa sun fito kan titunan birnin Kaduna domin neman adalci da gaskiya, inda suka bukaci hukumomi su tabbatar da an hukunta tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, kan zargin bacewar Dadiyata da aka dade ana yi.

 

 

Masu zanga-zangar sun taru a mahadar UTC a cikin birnin Kaduna, daga nan suka yi tattaki zuwa Gidan Gwamnati suna rera wakokin hadin kai tare da dauke da alluna masu dauke da rubuce-rubuce daban-daban, suna nuna bacin ransu kan yadda lamarin ya dade ba tare da warwarewa ba.

Daga cikin sakonnin da ke jikin allunan akwai: “Muna bukatar cikakken bincike na jama’a, a yi tantancewa yanzu”, “Malam Nasir El-Rufai, ina Dadiyata yake?” da kuma “Daukar nauyin zanga-zanga ba zai kare El-Rufai ba, dole ya fuskanci shari’a.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *