Ko daya ban tausayawa Ghali Basaf da Shehu Wada Sagagi ba da aka sutalesu daga kujerunsu.

A rayuwa dole mutum ya zama mai tsayayyen ra’ayi, hakanan kuma wajibi ne mutum ya shiryawa karbar sakamakon matakin da ya dauka a rayuwarsa, mai kyau ko kuma akasin haka.

“Idan da ni ne Basaf ko ni kadai zan zauna da Kwankwaso cikin ciyamomi ba zan koma APC ba, hakanan idan da ni ne Sagagi ana batawa tsakanin jagora da gwamna zan ajiye masa kujerarsa na kara gaba.

” Ita amana guda daya ce a duniya, kuma ba a kullawa da mutum sama da guda daya, musamman masu mabambantan ra’ayi a lokaci daya.

“Yaudarar kai ne Basaf yace wani zai yarda da shi ba Kwankwaso ba, hakanan Sagagi tsananin yaudarar kai ne kawai zai zaunar da shi a gwamnati bayan komawar gwamna APC.

” Sai dai duk da wannan duk su biyun ina musu ban gajiya tare da fatan alkhairin dawowa gidansu kuma gidan gaskiya a siyasar Nigeria.

” Yanzu dai duk sai mu dunguma mu koma ADC mu marawa jagoranmu Kwankwaso baya yayi nasara da karfin ikon Allah,”

~Aminu~

In ji Dr. Aminu Tukur Adam, ɗan Kwankwasiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *