Aƙalla mutane biyar daga gida ɗaya sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a jihar Yobe.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, kuma ya shafi mazauna ƙaramar hukumar Potiskum, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin jimami.
Wani ɗan uwan mamatan, Dahiru Musa Talba, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wani rubutu da ya yi a Facebook. Ya bayyana cewa mutane biyar daga cikin danginsu sun mutu a hatsarin, yayin da wasu uku suka jikkata da raunuka daban-daban.
A cewarsa, an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Damaturu, babban birnin jihar Yobe, inda ake kula da su a yanzu.
Ya bayyana lamarin a matsayin mai matuƙar tayar da hankali, yana mai nuna baƙin cikin rashin da akayi .
Ya ƙara da cewa hatsarin ya faru ne a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, wadda aka sani da yawan zirga-zirgar ababen hawa.
Jami’in hulɗa da jama’a na ’yan sandan jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mutane biyar sun mutu, yayin da wasu suka jikkata.
Ya ce ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin hatsarin.
“Hatsarin ya shafi ’yan gida ɗaya. Mutane biyar sun mutu, yayin da wasu suka samu raunuka daban-daban,” in ji shi.
An bayyana sunayen mamatan da Hajjagana Dahiru Zayi, Ibrahim Dahiru Zayi, Muhammad Dahiru Zayi, Hauwa Dahiru Zayi, da wani ɗan gidan nasu.
Shi ma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jajanta wa mahaifin mamatan, Alhaji Mohammad Dahiru Zayi, bisa wannan babban rashi.
A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na wamnan, Malam Mamman Muhammad ya fitar, gwamnan ya ce ya samu labarin cikin baƙin ciki sosai, yana mai bayyana hatsarin a matsayin “mai firgitarwa, mai tayar da hankali da kuma mai raɗaɗi.”
Haka kuma gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya ba iyalan da suka rasa ’yan uwansu haƙurin jure wannan babban rashi.
