Jahar Ogun Ta Bada Hutun Ranar Juma’a Domin Rajistar Katin Zaɓe

Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.

Gwamnan Jahar Ogun, Dopo Abiodun ya ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu domin baiwa ma’aikata damar yin Rajistar Katin zaben da ke gudana.

Wakilin Majiyar Jakadiya, ya bada rahoton cewa, wannan shine hutu na biyu a cikin satin ɗaya, da Gwamnan ya baiwa ma’aikata damar yin rajistar Katin Zaɓe.

Tun da farko dai Abiodun, ya bayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu adukkan fadin jahar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da Sakataren Yan jarida , Kunle Somorin ya fitar ranar Alhamis a Abeokuta, ya bayyana cewa, sanarwa ta biyo bayan yawan mutane aka samu wanda suka isa rajistar Zaɓe a ranar Talata, kuma mutane da dama na cigaba da zuwa cibiyoyin rajistar zaɓe, a yayinda zai ƙare a ranar Lahadi, 31 ga watan Juli.

Gwamnan yace “sake bada hutun, ya zama dole domin bada dama ga dukkanin Ma’aikata a Jahar da basu kammala rajistar, a yayinda aka samu mutane da yawa suka fito, tun bayan farawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *