Kamfanin dillancin labaran kasar sudan ya ruwaito cewa, Gwamnatin mulkin sojin kasar ta bayyana cewa, ta kafa wani kwamitin da zai gudanar da bincike kan rikicin da aka samu a jihar Blue Nile a baya bayan nan, wanda ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 200 tare da raba dubbai da muhallan su.
A makon da ya gabata, Rayhaan Radio ta ruwaito yadda aka kashe mutane da dama, biyo bayan wani rikicin kabilanci da ya barke tsakanin Kabilar Hausawa da kuma wasu kabilu dake kasar.
Kakakin rundunar sojin mulkin kasar Kanar Nabil Abdullah ya ce, kwamitin zai gudanar da binkice tare da duba lamurorin tsaro a yankin.
Kazalika Gwamnatin Mulkin sojin kasar ta kuma kafa wata runduna ta musamman a jiihar ta Blue Nile domin lalubo hanyoyin da za’a magance rikicin kabilancin.
Kazalika ko a ranar Juma’ar data gabata sai da Sojojin kasar, suka sanya dokar ta baci a jihar domin shawo kan rikicin.
