Bayan Naɗa Hadimai 50,000, Gwamna Wike Ya Aika Sunayen Sabbin Kwamishinoni 18 Ga Majalisa

Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya mika sunayen kwamishinoni 18 ga majalisar Dokoki domin tantancewa tare da amincewa dasu.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun magatakardan Majalisa, Stanford Oba, ta gayyaci wadanda aka naɗa, da su bayyana a gaban Majalisar a ranar 25 ga Oktoba (yau) don tantancewa.

Wadanda aka ambata a jerin sunayen sun hada da Farfesa Princewill Chike da Jacobson Nbina da Mista Ndubuisi Okere da Mrs. Inime Aguma da Charles Amadi da Mrs. Tonye Oniyinde Briggs da Mista Ben Daminabo da Mista Chris Finebone da Austin Ben Chioma da Mista Uchechukwu. Nwafor.

Sauran sun hada da Dr. Fred Barivule Kpakol, Emenike Eke, Mista Prince Ohia, Farfesa Kaniye Ebeku, Mista Ezekiel Agri, Misis Ukiel Oyaghiri, Damiete Herbert Horsfall da Emeka Onowu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *