Atiku Ne Keda Shirin Wargaza Najeriya, Ba Tinubu Ba – Martanin Keyamo Ga Obasaki

Karamin Ministan Ƙwadago da samar da ayyukan yi Festus Keyamo a ranar Talata ya ce jam’iyyar PDP da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na shirin wargaza Najeriya.

Keyamo yana maida martani ne kan kalaman Gwamna Godwin Obaseki na cewa Najeriya za ta wargaje idan jam’iyyar All Progressives Congress, APC, dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, ya zama shugaban kasa a 2023.

Obaseki ya shawarci ‘yan Najeriya da su guji goyon bayan APC a 2023.

Gwamnan ya ce nan ba da jimawa ba bashin Najeriya zai kai Naira tiriliyan 60, lamarin da zai shafi tsararraki.

Da yake mayar da martani, Keyamo bai amince da Obaseki ba, yana mai jaddada cewa Atiku ne ke son raba Najeriya.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya tuno yadda Atiku ya ce Najeriya ba ta bukatar shugaban Yarbawa, Igbo, ko kuma Hausa-Fulani.

A cewar Keyamo, kalaman Atiku na da nufin wargaza kasar ne.

Ya ce: “Malam, ban yarda ba. Dan takarar ku da ya riga ya nemi ’yan Arewa da kada su zabi ’yan takarar Yarbawa ko Igbo wanda kuma ke yi wa Shugabancin Kudu-maso-Kudu da Kudu-maso-Gabas alkawari a 2027 ko 2031 ta hanyar hawainiya, shi ne wanda ke son wargaza Nijeriya. Chikena.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *