Babu Kokwanto Mu Zamu Karɓe Iko Da Jam’iyyar PDP ta sha alwashin lashe jihohi 25 ciki har da jihar Legas a babban zaben shekara mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya bayyana haka a wani taro a Abuja domin karbar rahoton kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP na jihar Legas da Osun.
“PDP za ta samu gwamna a Legas da wasu mukamai da dama a majalisar dattawa, da wakilai, da na majalisu Dokoki na Jihohi,” in ji Ayu.
Ya kuma bukaci shugabannin jam’iyyar da ke da matsala da su warware irin wadannan matsalolin, inda ya ce idan aka yi hakan, jam’iyyar PDP za ta yi murna, kamar yadda na yi hasashe, akalla gwamnoni 25, sannan kuma za su samu babbar nasara a jam’iyyar.
A cewar Ayu, yayin da jam’iyyar a Legas ke cikin rudani, aikin da kwamitin da Cif Eyitayo Jegede ke jagoranta ya yi ya kara haskaka damar da PDP za ta samu a zaben badi.
