Kotu Ta Yanke Ma Wadume Fitaccen Mai Garkuwa Da Mutane Daurin Shekara 7 a gidan Gyaran Hali
Kotu a Najeriya, ta yanke wa fitaccen mai garkuwa da mutane Hamisu Bala mai inkiya Wadume, hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari bayan samun shi da samun shi da laifin satar mutane domin karbar kudin fansa.
Popular News Hausa ta ruwaito cewa, mai shari’a Binta Murtala Nyako ce yanke hukuncin, ta kuma samu Wadume da laifin tserewa daga hannun jami’an tsaro tare da yin mu’amala da manyan makamai ba tare da izini ba.
