INEC Tace APC Bata Ƴan Takara A Kujerar Lawal Da Kuma Akwa Ibom

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta ce jam’iyyar APC ba ta da dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa da Akwa Ibom Arewa maso Yamma.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, mai wakiltar Yobe ta Arewa na fafutukar samun tikitin jam’iyyar bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC. A gefe guda kuma, tsohon gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio shi ma yana fafatukar neman tikitin jam’iyya mai mulki ta tsayawa takarar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma. Akpabio ya kuma nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Sai dai kwamishinan hukumar INEC na kasa, Festus Okoye ya ce hukumar zabe ba ta amince da duk wani dan takarar jam’iyyar APC na shiyyar sanatoci biyun ba.

“A wadannan mazabu guda biyu an gabatar da sunaye guda biyu kuma hukumar ta yanke shawarar cewa sunayen ba mutanen da suka fito daga sahihin zaben fidda gwani na jam’iyyar ba ne kuma ba mu buga sunayensu ba.” Inji Okoye yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a shirin Sunday Politics.

Ya kara da cewa, “APC ce ta saka sunayen su (Lawan da Akpabio) zuwa cibiyar ‘yan takarar mu amma hukumar ta yanke shawarar cewa ba su ne ‘yan takarar da suka fito daga sahihin zaben fidda gwani na jam’iyyar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *