Dan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar PDP ya Alhaji Atiku Abubakar da abokin takararsa, Dakta Ifeanyi Okowa, ya kara samun karbuwa ya yin da mataimakin shugaban jam’iyyar LP a jihar Oyo magajin garin Olubukola Olayinka ta koma jam’iyyar ta PDP a hukumance tare da dariruwan magoya bayanta.
Da take bayyana ficewarta daga tsohuwar jam’iyyar ta, Olubukola ta ce yakin neman zaben Atiku da Okowa na tabbbatar da shugabancin Kasa a 2023za a cimma nasara.
Ta bayyana gazawar gwamnatin tarayya ta yanzu ta wajen magamace babbar mamufar mulki.
A yayin da take sukar shugabancin jam’iyyar LP a jihar ta bayyana Atiku a matsayin wanda ke da hazakar siyasa gogewa da kyma kishin kasa wajen hada kan ‘yan Najeriya.
“Kasancewar tsohon mataimakin shugaban Kasar nan Atiku Abubakar tsohon shugaban hukumar Kwastom shi ne dan takara daya tilo a tsakanin sauran yan takarar da ke da manufar siyasa don dawo sa martabar kasar nan da hadin kan da ta rasa” inji ta.
