Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari a wani masallaci da ke ƙauyen Ga Allah Babba na ƙaramar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
A yayin harin an samu rasa ran babban limamin masallacin da wasu mutane biyu sai kuma wasu masu ibada biyu da suka samu raunuka.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ake gudanar da sallar asuba kamar yadda wani mai suna Zubair Abdurrauf ya shaida wa manema labarai na gidan TV na Channels.
