Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari.
Gwamna Gboyega Oyetola na Jahar Osun ya rasa Akwatin gidan Gwamnati, na Akwatin Osogbo, ga Sanata Ademola Adeleke a zaɓen Gwamna dake wakana a halin yanzu.
A yayin da Adeleke na Jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’u 117 a mazabar Agowande /Oshogbo GRA, Akwatin zabe dake ofishin gwamna, inda abokin Takarar sa na Jam’iyyar APC Oyetola ya samu kuri’a 106.
Akwatin zaben yana cikin Ƙaramar Hukumar Olorunda.
Masana na ganin cewa wannan wata manuniya ce dake nuna cewa Jam’iyyar APC Zata sha kaye a zaɓen Gwamna dake wakana
