Da Ɗuminsa: An Kwantar Da Osinbajo Asibiti, An yi Mashi Tiyata
A yanzu haka mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yana kwance a asibiti domin yi masa tiyata.
Babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Laolu Akande, ne ya bayyana hakan a yammacin ranar Asabar.
“A yau ne mataimakin mataimakin shugaban kasa Osinbajo yake kwance a asibiti domin yi masa tiyata saboda yawan jin zafi da ya samu a kafa wanda ya samu rauni a lokacin da yake buga wasa. Likitocinsa za su ba da karin bayani, game da yanayin jikin nasa daga baya a yau, ”ya wallafa a shafin Twitter
