Gwamnatin Katsina Zata Saki Yan Fashin Daji 70 Da Aka Kama

Gwamnatin jihar katsina karkashin jagorancin Dikko Radda, ta bayyana cewa yanzu haka tana kan shirye-shiryen saki ‘yan fashin daji guda 70 da aka kama da zargin aikata laifin ayyukan ta’addanci kuma suke fuskantar shari’a.

Gwamnatin ta bayyana yunkurinta na sakin mutanen a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin inganta yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ƙungiyoyin yan ta’adda masu ɗauke da makamai da sauran al’umma gari a faɗin jihar.

Rahotanni sun ruwaito cewa, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Nasir Mu’azu Danmusa ya ce an yanke wannan shawara ne don karfafa zaman lafiya da aka cimmawa tsakanin al’ummomin da abin ya shafa da kuma yan fashin da suka tuba.

Saidai Kwamishinan ya kara fadada bayani musamman yadda mutanen jihar ke ci gaba da nuna rashin jin dadinsu dangane da sakin yan fashin da Gwamnatin ke yunkurin yi.

Ya ce yanzu haka yarjejeniyar zaman lafiyar aka samu a kananan hukumomi da lamarin ke faruwa, ya haifar da sakin mutane kusan 1,000 da aka sace a cikin al’ummomi da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *