Hukumar kiyaye haddura ta FRSC reshen jihar Kano ta gargadi direbobin motocin haya da su kiyaye dokokin tuki yayin bukukuwan Sallah domin kaucewa hadurran mota.
Hukumar ta kuma bukaci direbobin su guji lodin wuce gona da iri, gudun wuce kima da kuma tuki cikin ganganci ko rashin kulawa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in wayar da kan jama’a na hukumar a jihar, Abdullahi Labaran, ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce kwamandan FRSC na jihar Kano, Idris Lawal, ya yi wannan kira ne yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da aka gudanar a kan titin Kano zuwa Zariya.
A cewar sanarwar, an shirya gangamin ne bisa umarnin hedikwatar FRSC domin gudanar da kamfen na kasa baki daya na wayar da kan jama’a kafin bukukuwan Sallah na shekarar 2026.
A yayin shirin, kwamandan ya ziyarci tashar motar Kano Line da ke kan titin Kano–Zariya, inda ya gana da kungiyoyin masu harkar sufuri da suka hada da kungiyar direbobin mota ta kasa (NURTW), kungiyar masu motocin sufuri (NARTO) da kuma kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (RTEAN), tare da direbobi da fasinjoji.
