Mutane 1,040 Daga Shiyyar Funtua Kowane Ya Samu Tallafin Dubu 30 Daga Kungiyar TDA

kungiyar nan ta Tinubu/Dikko Assured 2027, TDA, karkashin jagorancin shugabanta, Umar Ahmad Zayyan, ta raba tallafin kudade ga masu kananan sana’o’i na nera dubu talatin ga kowane mutum har su 1040.

Taron Wanda ya kunshi gaba dayan kananan hukuminin shiyyar Funtua ya waka ne a ranar Alhamis a karamar hukumar ta Funtua.

Da yake jawabi a wajen taron shugaban kungiyar TDA 2027, Umar Ahmad Zayyan, ya bayyana cewa shirin bayar da tallafin na daga cikin muhimman kudirorin kungiyar na tallafawa jama’a musamman masu kananan sana’o’i, don ingata tattalin arziki.

Haka kuma Zayyan ya kara da cewa shirin na tafiya ne daidai da manufofin Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda da kuma shugaba Tinubu na inganta rayuwar al’umma.

A jawabin Gwamna Dikko Radda wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Lafiya, Musa Adamu Funtua, ya yaba wa kungiyar Tinubu/Dikko Assured, bisa namijin kokarin da take wajen taimakon talakawa da shimfida ayyukan alheri a fadin jihar Katsina.

Shi ma kodinetan kungiyar, Khalil Ibrahim Aminu ya bayyana Umar Zayyan a matsayin mutum jajurtacce wanda ya tafiyar da rayuwarsa da al’amuransa ga shimfida ayyukan alheri.

Suma Wadanda suka samu tallafin sun nuna godiya da jin dadinsu tare da alkawarin tafiyar da kudin ta hanyar da ya dace.

Taron ya samu halartar manyan mutane daga ɓangarorin jihar Katsina, da suka hada da Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtua da Engr. Muttaqha Rabe Darma, da manyan malaman jami’o’i da shubannin kungiyar Tinubu/Dikko Assured 2027.

Irin wannan tallafi dai kungiyar ta TDA tuni ta riga ta gudanar da shi a shiyyoyin Daura da Katsina kafin wannan na shiyyar Funtua da ta shirya a ranar Alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *