A Da Ba A Ga Maciji: Haɗuwar Gwamnoni 3 Na Katsina A Wuri Guda

Siyasa ba da gaba ba: Gwamnoni uku sun hadɗu wuri guda a Katsina.

A ranar 2-12-2023 jami’ar gwamnatin tarayya da ke ƙaramar hukumar Dutsinma a jihar Katsina a Najeriya, tayi bikin yaye dalibai gami da karrama wasu muhimman mutane da ke bada gagarumar gudumawa ga cigaban al’umma.

Bikin ya samu halartar muhimman mutane daga bangarori daban-daban a faɗin ƙasar, kama daga masana ilmi da dalibai da masu mulki da Ƴan siyasa da Ƴan kasuwa da sauran mutane maza da mata a fannonin rayuwa.

Daga cikin muhimman mutanen da aka karrama da digirin girmamawa a wurin taron, sun hada da tsohon gwamnan jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema, da mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar, da kuma Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Wani abun burgewa da ban sha’ awa shine yadda gwamnan jihar Katsina mai ci Malam Dikko Umaru Radda PhD, da gwamna mai barin gado Rt Hon. Aminu Bello Masari, suka yi wa takwaransu tsohon gwamnan jihar Barista Ibrahim Shehu Shema kara bisa ga karamcin da jami’ar ta FUDMA ta yi ma shi.

Barista Ibrahim Shehu Shema shine ya gaji marigayi tsohon gwamnan jihar Katsina kuma tsohon shugaban ƴasar Najeriya, Malam Umaru Musa Yar’adua da ya yi gwamnan Katsina daga shekarar 1999-2007 a karkashin tutar Jam’iyyr PDP, a sa’ilinda Barista Ibrahim Shehu Shema ya kasance gwamna daga shekarar 2007-2015 shima daga jami’yyar PDP, inda daga bisani Rt. Hon Aminu Bello Masari zama gwamnan jihar a karkashin tutar Jam’iyyr APC daga shekarar 2015-2023, sai gwamna mai ci Malam Dikko Umaru Radda ya karbi ragamar mulki a shekarar 2023 Shima a tutar Jam’iyyar APC.

Abun lura anan shine yadda kowane daga cikin Gwamnonin su da magoya bayansu suka haɗu wuri guda cikin murna da farin ciki da annaushuwa, ba tareda sai’nsa ko jifar juna da kalaman batanci ko baƙaƙen maganganuba.

Wannan na nuni ƙarara cewa salon siyasar jihar Katsina tasha bamban da siyasar wasu jihohin ƙasarnan, sannan Kuma wata manuniyace ta nuna soyayya da yan’uwan tare da kaunar juna dake tsakanin Katsinawa da makwabtansu da sauran al’ummar ƙasar. Hakan ya tabbatar da kirarin nan da ake yiwa jihar Katsina da cewa Katsina ta Dikko Ɗakin Kara.

Sannan kuma hakan na nuni da cewa, siyasar jihar Katsina, na ci gaba da kasancewa zakaran gwajin dafi da kuma zamo wa abun koyi a salon siyasar arewaci dama kudancin ƙasar dama nahiyar Afrika bakiɗaya.

Abdulaziz Salisu
4/12/2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *