Mutum Miliyan Huɗu Zasu Samu Ilimin Kwamfuta Kyauta A Katsina

Shirin DIGIKAT: Al’umar jihar Katsina milyan hudu zasu ci gajiar ilmin na’ura mai kwakwalwa a cikin harshen Hausa kyauta.

Al’umar jihar Katsina milyan hudu ne zasu amfana da ilmin na’ura mai kwakwalwa kyauta acikin sheharu hudu zuwa biyar masu zuwa.

Jamiin kula da shirin DIGIKAT Muhammad Abbas Usman ya bayyana haka alokacin kaddamar da Shirin,wanda sakataren gwamnatin jihar Katsina Alhaji Abdullahi Garba Faskari yayi a dakin taro na masaukin shugaban Kasa dake tsofon gidan Gwamnatin jihar Katsina.

Muhammad Abbas Usman ya bayyana cewa ayanzu haka shafin yanargizo na shirin DIGIKAT a bude yake domin yin rijistar mutun dubu goma shabiyar a kashin farko na shirin.

Yace dukanin mai shaawar shiga shirin zai iya shiga shafin nasu awayar hannu ta Android domin zabar kwasa- kwasan da mutum ke shaawa kwarewa akai.

Shugaban kula da shirin na DIGIKAT ya Kara dacewa a kasashin farko na shirin, yankasuwa da ma’aikatan gwamnati da malaman makaranta da dalibai nada damar shiga shirin domin amfana.

Muhammad Abbas Usman ya cigaba da cewa sauran bangarorin da Shirin DIGIKAT zai baiwa fifiko sunhada shirin kulada lafiya ta hanyar wayar hannu, da koyar da dabarun noma na zamani, da sauran muhimman bangarori na rayuwa.

Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Alhaji Abdullahi Garba Faskari, wanda yasamu wakilcin Daraktan yada labaru na ofishin sa Alhaji Abdullahi Aliyu Yar’adua ya yaba da hangen nesan matasan na marawa kwazon Gwamnati baya, sannan ya bayyana matasan a matsayin abokan tafiya ta fuskar samar da cigaba.

Sauran wadanda sukayi jawabi a lokacin kaddamar da Shirin sun hada da mashawarci na musamman ga shirin Dr. Muttaka Rabe Darma da Sirajo Aliyu(Associate Professor) kuma shugaban kungiyar masu aiki da n’aura mai kwakwalwa ta Kasa, da Dr. Bashir Kurfi, da shugaban Shirin na DIGIKAT. Usman Ishak Karofi da shugaban shirin na DIGIKAT. Sanusi Muhammad Sulaiman da Abdulrahman Mustapha da Adnan Muhammad.

Dukkansu sunbukaci al’ummar jihar Katsina dasu bada goyon baya ga shirin ta hanyar yin rijistar domin samar da cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *