Wata kotu da ke zamanta a Abuja ta wanke Hon. Ado Doguwa bisa zarginsa da ake da hannu a kisan kai a lokuttan zaɓen shekarar 2023.
Bayan wanke Hon. Ado Doguwa da kotun ta yi, ta kuma ci tarar Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, naira miliyan 25 da ta ce a Hon. Doguwa a matsayin diyyar ɓata ma sa suna da aka yi.
Kafar sadarwar Liberty ta ruwaito cewa, bayar da ummurnin da kotun ta yi ga gwamnan Kano ya biyo bayan ɗaukaka ƙara da ya yi dukda wata kotu a Kano ta ce ba ta ga hujjojin da zata kama Ado Doguwa da su ba.
