Akwai Rashin Hankali Ga Wanda Yace Najeriya Lafiya Ƙalau Take – Obasanjo
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce duk wanda ya ce Najeriya na da kyau akwai bukatar a duba lafiyar sa, yana mai cewa bai kamata kasar ta kasance a inda take a halin yanzu ba.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Larabar da ta gabata a wajen taron lacca na shekara 15 na gidauniyar Wilson Badejo a Legas.
“Najeriya ba inda ya kamata ta kasance a yau. Idan wani ya ce babu laifi a inda muke a halin yanzu, to ana bukatar a duba kan mutumin ko yana da motsi,” in ji Obasanjo.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi zabin da ya dace a zabe mai zuwa domin a daidaita al’amura.
