Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Ɗan Shekara 3, Ta Lalata Gidaje 100 A Jahar Gombe

Daga Wakiliyar Mu Amira Salisu Batsari

Wani yaro Dan Shekaru 3 ya rasa ransa yayin da Dan Uwansa Mai shekaru 2 ya samu munanan raunika biyo bayan wani Mamakon Ruwa da sanyin safiya daya haddasa zaman ɗar-ɗar a garin Bajoga dake Ƙaramar Hukumar Funakaye ta Jahar Gombe.

Mamakon Ruwan daya ɗauki kimanin awanni biyar a ƙarshen sati ya haddasa Ambaliyar Ruwan wanda yayi sanadiyyar faduwar bangon dakin da yara biyu ke ciki na barci a Unguwar Fada kusa da Fadar Sarki.

Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa, Mutane da dama sun samu raunika, kuma suna cigaba da karɓar magani a Babbar Asibitin Bajoga, da sauran Asibitoci.

Wani Mazaunin yankin Bajoga, Yahaya Haruna ya shaidawa Majiyar Jaridar Jakadiya cewa, Ruwan saman ya fara sauka da misalin ƙarfe 5:30 na safe, har zuwa Karfe 11:00 na safe, a dai – dai lokacin da mutane suka samu raunika yayin da sama da gidaje 100, Dabbobi da kayayyakinsu da kuma dimbun Miliyoyin Nairori suka Lalace, Musamman a yankin Shara-mansur da Badoriyel na garin.

Har zuwa lokacin haɗa wannan Rahoto, Shugaban Bada Ceto na Hukumar Bada Agajin Gaggawa (SEMA), Muhammad Garba ya bayyana cewa, Har yanzu suna garin Bajoga, domin binciken yadda lamarin ya faru da kuma sanin ainihin iyakar gidajen, da Dabbobi, da kuma kayayyakin da ambaliyar ruwan ya Lalata.

Haka Zalika, Gwamnan Jahar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya jajantawa iyalan waɗanda suka mutu da sauran waɗanda suka samu raunika da kuma waɗanda suka rasa Dukiyoyin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *