Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis din nan a jihar Legas ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi imani da karfin da sojojin kasar ke da shi wajen kiyayewa da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
Da yake bayyana buda wasannin sojojin ruwa na Najeriya karo na 12, na LAGOS 2022, shugaban kasar ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa dakarun sojin kasar za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na tsawon lokaci domin dakile kalubalen tsaro a kasar.
Ya ce hukumomin tsaro za su ci gaba da tabbatar da cewa an samar da dukkan matakan da suka dace domin kare lafiyar ‘yan Najeriya.
Shugaban ya kuma sake jaddada mahimmancin hadin gwiwa tsakanin sojoji da sauran hukumomin tsaro da sauran al’umma domin samar da zaman lafiya da tsaro.
Shugaba Buhari wanda ya kuma kaddamar da sabon rukunin wasannin motsa jiki na sojojin ruwa da aka gina a Najeriya, ya yabawa babban hafsan sojin ruwa, bayis Admiral Awwal Gambo, bisa yadda yake saka hannun jari a harkokin wasanni.
”A cikin shekarun da suka gabata, wasanni sun kasance kayan aiki don ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin sojoji, da sanya ladabtarwa da shirye-shiryen yin aiki tare a cikin soja. Ina da yakinin cewa wadannan wasannin za su haifar da dandali ga sojojin ruwan Najeriya don cimma wadannan manufofi da sauransu.
