Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
Kimanin mutane ukku suka rasa rayukansu yayin da sama da mutane dari biyar suka rasa muhallinsu sanadiyar ballewar Kogin Niger da Benue inda ya mamaye Ƙaramar Hukumar Ibaji dake jihar Kogi.
Dan majalissa mai wakiltar Ibaji a Majalissar Dokoki Hon. Atule Egbunu ya tabbatar da faruwar lamarin a yayin wata tattaunawa da akayi dashi a Lokoja a daren ranar Laraba.
Acewar Egbunu, ambaliyar ta shafe dubban Gidaje da Gonaki, ya kuma kwantata lamarin a matsayin annobar shekara.
Ya bayyana cewa annobar ta haifar da wahalar samar da wurare da za’a sanya m wadanda lamarin ya shafa.
Dan majalissar yayi kira ga Gwamnatin Jihar da Gwamnatin tarayya da sauran Ƙungiyoyin Bada Tallafi na Duniya dasu kawowa al’ummarsa ɗauki.
