Lauyoyin gwamnatin Kano sun janye yajin aiki

Ƙungiyar lauyoyin gwamnati ta Najeriya, wato Law Officers Association of Nigeria (LOAN), ta janye yajin aikin da ta fara yi a jihar Kano.

Shugaban ƙungiyar LOAN na jihar Kano tare da shugabannin ƙungiyar ma’aikata ta Trade Union Congress (TUC) ne suka sanar da dakatar da yajin aikin, bayan shafe sa’o’i ana tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu tare da cimma matsaya.

A yayin ganawar, gwamnatin jihar Kano ta samu wakilci daga wasu manyan jami’ai uku, ƙarƙashin jagorancin mukaddashiyar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota. Sauran wakilan sun haɗa da Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, da kuma Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin
Gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana godiyarsa ga shugabannin LOAN, TUC da sauran masu ruwa da tsaki da suka taka rawa wajen cimma wannan matsaya.

Ya ce irin wannan haɗin kai da nuna kishin ƙasa, nauyin aiki da kuma balaga ne suka taimaka wajen kawo ƙarshen takaddamar.

A cewarsa, wannan na nuna cewa manufofin gwamnatin jihar Kano na “Kano First” na ci gaba da haifar da sakamako mai kyau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *