Ba Za’a Taɓa Mancewa Da Gudunmawar Da Ka Bada Ga Ƙwallon Ƙafa – Saƙon Ta’aziyyar Buhari Ga Iyalan Pele
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya ce duniya ba za ta manta da gudunmawar da fitaccen dan wasan kwallon kafa na Brazil Edson Arantes do Nascimento ya bayar ba.
Dan wasa Pele ya rasu ne a juya Alhamis yana da shekaru 82 a duniya.
“Pele ya tafi amma duniya ba za ta taba mantawa da shi ba. RIP,” in ji wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, mai taken ‘Shugaba Buhari ya yi jimamin rasuwar fitaccen dan wasan kwallon kafa, Pele.
A jawabin da ya yi wa fitaccen dan wasan kwallon kafa a madadin daukacin ‘yan Najeriya, Buhari ya ce, “yana masa fatan dacewa.”
Buhari ya ce Pele ya gudanar da rayuwa mai kyau kuma ya ba da babbar gudummawa ga ci gaban kwallon kafa na duniya musamman da kuma wasannin duniya gaba daya.
“Ya kasance yana da karamci mai girma na ruhi da tawali’u duk da girmansa a matsayinsa na dan wasan ƙwallon ƙafa.”
“Ya kuma taimaka wajen samar da daidaito a tsakanin al’ummomi da kabilu da ma addinai.”
Ya kasance Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman.
Pele ya tafi amma duniya ba za ta taba mantawa da shi ba.
Pele ya lashe gasar cin kofin duniya sau uku kuma ya zira kwallaye sama da 1,281, ya zama alamar kwallon kafa ta asali a cikin dogon aiki wanda aka ba shi sunan “Dan wasan Karni” a cikin shekara ta 2000.
