Hukumar gasar Firimiya ta kasar Ingila ta dakatar da mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola daga buga wasanni biyu.
Wasannin da Guardiola na zai ja ragamar Man City sun hada da wasan da za.su buga da West Ham United a gasar Firimiya da kuma wasan zagayen na kusa da na karshe na gasar FA Cup da zasu buga a watan Afirilu.Hakan ya biyo bayan katin kora da ya samu a wasan da Manchester City ta doke Newcastle United da ci 3-1 a gasar cin kofin FA a jiya Asabar.
