Rashin ganin tauraron dan wasan Najeriya, Victor Osimhen, a cikin jerin ‘yan wasan da suka tafi Alanya domin fafatawa da Alanyaspor a gasar Ziraat Turkish Cup ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin magoya baya. Sai dai kulob din Galatasaray ya yi gaggawar bayyana cewa matakin wani bangare ne na shirin kula da lafiyarsa, ba wai wata matsala ba.
Kulob din ya bayyana cewa Osimhen yana kan wani tsari na atisaye na musamman domin farfadowa (active recovery), duba da yawan wasannin da yake bugawa a kakar wasa ta bana. Haka kuma, ba shi kadai aka ware ba, domin wasu fitattun ‘yan wasa kamar Uğurcan Çakır, Davinson Sánchez, Abdülkerim Bardakcı da Mario Lemina su ma an saka su cikin irin wannan tsari na musamman.
A cewar kulob din, wannan mataki yana nufin daidaita bukatar nasara a yanzu da kuma tabbatar da dorewar lafiyar ‘yan wasa a dogon lokaci, musamman wadanda suka dade suna taka leda a gasar lig, ta nahiyar Turai da kuma wasannin kasa da kasa. Duk da cewa Osimhen ya zura kwallaye 17 tare da bayar da taimako shida a wasanni 25 tun bayan zuwansa Istanbul, har yanzu bai fara taka leda a gasar Kofin Turkiyya ta bana ba, sakamakon rashin samunsa a wasannin baya saboda wakiltar Najeriya a gasar AFCON.
