Tsohon dan wasan kwallon kafa na Najeriya, Segun Odegbami, ya bayyana rashin amincewar sa da matakin da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta dauka na kwace kofin gasar AFCON ta shekarar 2025 daga hannun kasar Senegal tare da mika shi ga kasar Morocco.
Odegbami ya bayyana wannan hukunci a matsayin abin mamaki da kuma rashin adalci, inda ya ke ganin cewa bai dace a soke nasarar da aka samu a filin wasa bayan kusan watanni biyu da kammala gasar ba.
“Ba a taba ganin irin hakan ba a tarihin kwallon kafa. Ba za ka iya kwace kofin da aka lashe a fili ba bayan watanni biyu,” in ji shi
Odegbami ya bayyana cewa wannan shawarar ta haifar da bacin rai a tsakanin masoyan kwallon kafa da masu ruwa da tsaki a fadin duniya.
“Wannan hukunci ya girgiza sahihancin CAF. Ba abin mamaki ba ne yadda duniya ta tashi tsaye tana nuna rashin amincewa,” in ji shi.
Tsohon gwarzon dan kwallon Najeriyar ya nuna shakku kan manufar da ke bayan wannan mataki, inda ya bayyana shi a matsayin mai hadari kuma wanda bai dace ba.
