DAN wasan gaba na Super Falcons, Rinsola Babajide, ta bayyana cewa lashe gasar WAFCON X tare da Najeriya shi ne kololuwar nasarar da ta taɓa samu a rayuwarta ta ƙwallon ƙafa.
Ga Omorinsola Babajide, wadda ta taka leda a ƙasashe da dama tun daga haihuwarta a Landan har zuwa sauya sheƙarta daga Ingila zuwa Najeriya a 2021, babu wata nasara da ta kai ɗaga kofin Afirka tare da Super Falcons a 2024, abin da ta ce ya tabbatar da juriyarta, imaninta da sadaukarwar da ta yi tsawon shekaru.
Babajide ta taka rawar gani tun a matakin rukuni inda ta ci ƙwallo tare da bayar da taimako a wasan da Najeriya ta doke Tunisiya, kafin daga bisani ta zama ɓangare na tarihin dawowar da Super Falcons suka yi a wasan ƙarshe da Morocco, inda suka juya rashin nasara ta zama nasara tare da lashe kofinsu na 10 a nahiyar Afirka.
