Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar Jigawa (JSC) ta amince da tura wani alkalin kotun Shari’a, Sadisu Muhammad-Haruna, ritaya ta dole bayan samunsa da laifin cin hanci da kuma tsare mutum ba bisa ka’ida ba.
Daraktan Hulɗa da Jama’a da Tsare-tsare na hukumar, Abba Wangara, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Dutse, babban birnin jihar, inda ya ce matakin ya biyo bayan nazarin koke da kuma hujjojin da aka gabatar. Ya ce bincike ya nuna alkalin ya karɓi wasu kuɗaɗen da ba su cikin jadawalin kuɗaɗen kotun Shari’a na shekarar 2012, sannan ya tsare mai ƙorafi ba bisa ƙa’ida ba.
Hukumar ta ce wannan mataki gargadi ne ga duk wani jami’in shari’a cewa ba za ta lamunci cin hanci ko amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba, tare da sanar da cewa ta kuma amince da ƙarin girma ga sama da ma’aikata 80 da kuma naɗa wasu manyan ma’aikata a Kotun Ƙoli ta Shari’a ta jihar domin ƙarfafa ƙwazon aiki da ladafta nagarta.
