A wani gagarumin yunkuri na fadada samun kulawar lafiya, Gwamnatin Jihar Kano ta kuduri aniyar saka mutum miliyan daya masu karamin karfi cikin tsarin inshorar lafiya domin rage radadin kashe kudin jinya daga aljihunsu. Shirin na da nufin bunkasa damar samun muhimman ayyukan kiwon lafiya da kuma kare marasa galihu daga hadarin talaucewa sakamakon tsadar magani.
Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Kano, Kano State Contributory Healthcare Management Agency (KSCHMA), tare da hadin gwiwar National Health Insurance Authority (NHIA), za su aiwatar da rajistar ne karkashin Asusun Samar da Kiwon Lafiya na Farko (Basic Healthcare Provision Fund). An cimma matsayar ne a wani taro da aka gudanar a Kano, inda manyan jami’ai da masu ruwa da tsaki suka tattauna kan tsare-tsaren aiwatarwa, tantance masu cin gajiyar shirin da daidaita bayanai.
Sakatariyar Zartarwa ta KSCHMA, Rahila Muktar, ta bayyana cewa shirin wani babban mataki ne na kusantar cimma burin samar da cikakkiyar kulawar lafiya ga kowa (Universal Health Coverage) a jihar. Ta jaddada kudirin tabbatar da gaskiya da rikon amana yayin aiwatar da shirin, tana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage yawan kudin jinya da jama’a ke biya kai tsaye. A nasa bangaren, Kodinetan NHIA a jihar, Adamu Abdullahi, ya ce hukumarsu a shirye take ta bayar da goyon bayan fasaha da tsari domin tabbatar da cewa an bi ka’idojin kasa yadda ya kamata.
