Al’ummar wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Makarfi da ke jihar Kaduna sun maka shugaban ƙaramar hukumar, Garba Muhammad Sabongari a gaban babbar kotun tarayya bisa zargin kwashe kayan al’umma.
A takardar ƙarar da Daily Nigerian Hausa ta samu, wata ƙungiya mai suna GUBUCHI MOBILIZATION AND SOCIAL DEVELOPMENT (GUMSOD) ce ta kai karar shugaban ƙaramar hukumar.
A takardar ƙarar, ƙungiyar ta zargi shugaban ƙaramar hukumar da rufe famfunan burtsatse da kuma kwashe tankunan ruwa da kimar su ta kai Naira miliyan 60 ba tare da ya maido da su ko ya kawo wasu ba.
Ƙungiyar ta ce ƙauyukan da abun ya shafa sun hada da Hayin Gada, Rimin Gulma, Sabuwar Kasuwa, Tsamiyar Masau da Gidan Malama na Kwankwana, duk a ƙarƙashin garin Gubuchi.
Ƙungiyar ta koka cewa bayan rufe famfunan burtsatsen, al’ummar waɗannan garuruwa sun shiga matsalar ruwa da halin kunci, wanda ya sa ta kai shi kara domin a dauki matakin da ya dace.
Da mu ka tuntubi shugaban ƙaramar hukumar ta bakin hadimin sa na musamman akan harkokin solar, Muhammad Abdullahi, ya tabbatar da kwashe kayan.
Sai dai kuma ya ce an kwashe su ne da nufin gyara, amma kuma an dauki tsawon lokaci gyaran bai yiwu ba.
Ya baiwa al’ummar yankin hakuri, inda ya ce ana dafa da fara gyaran da nufin samar da isasshen ruwa ga yankunan da abin ya shafa.
