NSCDC A Jihar Katsina Ta Cika Hannu Da Wasu Mutane Su 4 Masu Kera Bindigun Gargajiya
Rundunar Tsaron Lafiyar Yan Kasa Reshen Jihar Katsina, ta chafke wasu mutane su 4 da suka shahara wurin kera bindigun gargajiya suna sayarwa ga al’umma ba bisa ka’ida ba.
Jami’in Hulda Da Jama’a na Rundunar SC Buhari Hamisu ne ya tabbatar da hakan ga Manema Labarai a Hedikwatar Rundunar da ke Katsina.
Wadanda aka chafke din su 4 an kama su ne a Masana’antar da suke kera bindigun da ke Kauyen Kore, kan hanyar Batsari, a cikin Karamar Hukumar Batagarawa.
Chafke mutanen ya biyo bayan rohoton sirri da Rundunar ta samu na yadda wadannan mutane ke aiwatar da cinikin kera bindigun, wanda ya sabawa doka da oda.
Accuracy News Hausa ta tsinkayi SC Buhari Hamisu yana mai cewa, Runduna ta Musamman ta RRS CE ta samu nasarar cika hannu da mutanen, biyo bayan umarnin Kwamandan Hukumar Dan Ile Moriki.
Kayayyakin da aka samu daga hannun su sun hada da manyan bindigu da suka fara kerawa guda 8 da kananan bindigu(Pistol) guda biyar da harsashen gargajiya da karafunan hada bindigun da kayan aiki sai mashina guda 2.
SC Buhari Hamisu ya yabawa jami’an akan wannan gagarumar nasara da suka samu, sai ya ce da zarar an kammala bincike za’a maka su gaban kotu domin fuskantar hukunci dai-dai da doka.
Daga nan sai ya nanata kudirin Rundunar na cigaba da yin bakin kokarin ta wurin cigaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyin gwamnati a fadin Jihar Katsina.
