Wani likitan Najeriya, Olawale Ogunlana, ya samu babbar karramawa bayan da aka saka shi cikin jerin masu kirkira 50 mafi tasiri a duniya na TikTok na shekarar 2026, abin da ya kara haskaka rawar da ‘yan Afirka ke takawa a fagen kirkire-kirkire na yanar gizo.
Kamfanin TikTok ya sanar da cewa Dokta Ogunlana ya fito a cikin TikTok Global Discover List 2026, wanda ke karrama masu kirkira a rukuni daban-daban kamar su Icons, Innovators, Foodies, Educators da Originators. An karrama shi a rukunin “Educators” saboda yadda yake saukaka bayanin cututtuka masu sarkakiya ta hanyar bidiyo masu kayatarwa, lamarin da ya mayar da dandalin sada zumunta tamkar asibiti na zamani wajen wayar da kan jama’a kan harkokin lafiya. A cewar shugaban kula da harkokin abun ciki na TikTok a duniya, James Stafford, jerin sunayen na 2026 ya kunshi mutanen da suka yi fice a cikin watanni shida da suka gabata ta fuskar ingancin bidiyo, yawan masu kallo, karuwar mabiya da tasirin da suka yi a duniya.
Da yake mayar da martani, Dokta Ogunlana ya ce wannan karramawa shaida ce ta yadda dandalan dijital ke sauya hanyar isar da sakonnin kiwon lafiya, yana mai cewa nasarar ba tasa kadai ba ce, illa babbar nasara ce ga sadarwar lafiyar jama’a a Afirka. Sauran ‘yan Afirka hudu da suka shiga jerin sun hada da Trevor Were daga Kenya da Wayne Chang daga Afirka ta Kudu a rukunin “Foodies”, sai Cherie Kihato da Tamia Nontsikelelo a rukunin “Originators”, wadanda su ma aka yaba da rawar da suke takawa wajen yada al’adunsu da kasuwancinsu ga duniya.
