An Yi ASarar Dukiyoyi Bayan Saukar Ruwan Sama Na Kimanin Sa’o’i 5 A Ekiti

Daga Amira Salisu Batsari.

Mafi yawan mazauna garin Ado Ekiti babbar birnin jihar Ekiti a ranar Lahadi ruwa ya afka gidanjensu sakamakon mamakon ruwan sama da aka sheka wanda ya dauki sa’o’i sama da shidda a daren ranar Lahadi.

Al’umma yankin unguwar Oshodi da Ilupeju Avenue da unguwar Ureje da unguwar Ita Eku da kuma Tamidire Eminrin da sauran unguwannin dake kusada hanyar makarantar kimiyya da fasaha sun asarar kayayyaki masu tsada.

An fara ruwan sama a ranar Lahadi da misalin karfe 10pm zuwa karfe 3:22am na ranar Litinin.

Lamarin dai yafi tsananta ga mazauna unguwar Temidire Emirin yayin da ruwa kogin Ureje ke gudu yana shiga bankuna inda ya hana dalibai da ma’aikata zuwa makarantu da wurin aikinsu a ranar Litinin.

Wani mazaunin Unguwar Temidire Emirin wanda ambaliyar ruwan ta shafa Mr. Jude Ajulo ya bayyana cewa suna cikin barci da misalin Karfe 2am kawai sai sukaji ruwa ya shigo inda yayi gaba da kayayyakinsu

Ajalu ya kara da cewa mazauna dakunan kwanan guda ukku sai suka fara gudu yayin suka ga ruwan yana shirin hallaka rayukansu.

Ya bayyana cewa” wannan dama yana faruwa a kowace shekara. Hakan ta faru a yan shekaru da suka gabata kafin mulkin Mr. Ayodele Fayose inda ambaliyar ruwan ta balle magudanan ruwan Ureje.

“Hanya da Gwamnati kawai zata taimakemu shine tayi mana magudanan ruwan da zai iya daukar ruwan da ya taho daga Odo-Ada da Oshodi da Ilupeju Avenue.

” Bai kamata ace anbar hakan na cigaba da faruwa ba saboda abin bacin Raine ace duk lokacin da akayi ruwa mai yawa muna ace rayuwarmu da kayyakinmu na shiga cikin garari.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Mr. Olajide Borode ya bayyana cewa hukumar ta fara ziyarartar yankunan da abun shafa domin samun ingantattun bayanai dangane da lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *